Ƙasar Yarbawa Kiɗan Bata

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ƙasar Yarabawa Kiɗan Bata


Gabatarwa

Kiɗan Bata, yana daga cikin kaɗe-kaɗe mafiya shahara a cikin dukkan kaɗe-kaɗen Ƙasar Yarabawa; da ke Kudu Maso Yammacin Najeriya. Duk da cewa amfanin kiɗan ya keɓantu da masu bautar Egungun (David, 2018). Sai kuma masu bautar Sango; wato allan tsawa da kuma masu rawar gargajiya ta dodon eleegun da suke cashe rawarsu da zarar an kaɗa gangunan Bata a lokutan bukukuwan yin sadaka da kuma bukukuwan binne gawarwakin tsofaffin cikinsu, kamar yadda ya zo a ruwayar Oluga da Babalola (2012). Shi kuwa Adedeji (2005), ya saka kiɗan na bata a cikin jerin karɓaɓɓun kaɗe-kaɗen gargajiya na addinin Kirista a Ƙasar Yarabawa.


Gangar Bata
Hoto:Music Africa Awake.

Bunƙasa

Sauyin zamani da kuma buƙatar faɗaɗa al’adun gargajiya tare da taskace su, sun saka samuwar wasu ƙungiyoyin kaɗe-kaɗen gargajiya suna amfani da gangunan bata, (Ogula da Babalola, 2012). Kiɗan yana faɗaɗuwa zuwa ga gamagarin kiɗa saboda sha’awar da jama’a (Yarabawa) suke da ita wajen yin kiɗan cikin al’amuran walwala da jindaɗin jama’a da ke gudana yau da kullum, kamar yadda David (2018), ya bayyana. Ya ci gaba da cewa ana kaɗa gangunan Bata a lokacin hidimar ƙungiyar bautar Egungun da kuma lokacin bukukuwan ‘yan ƙungiyar, amma saboda ɗaukaka da kiɗan ke samu a tsakanin jama’a ya fara zama gamagari.

Siffar Gangar Bata

Ganga ce da ake sassaƙa jikinta da itace cikin siffar zunguru da itacen bishiyar apa, sannan kuma a rufe bakinta da fatar ɗan-akuya. Haka kuma akan iya sassaƙa guda uku masu zagayayyira siffa (rounded) a ɗaure su waje guda.


Gangar Bata Mai Uku

Gangunan Bata

Kiɗan Bata yana da ayarin ganguna guda huɗu ko kuma guda uku da ake ɗaure su a tare (David, 2018; Oluga da Babalola, 2012):

  1. Iya-ilu Bata: Ita ce uwar-garke a cikin ayarin waɗannan ganuguna.
  2. Omele-abo/Emele-abo Bata: Macen gangar bata.
  3. Omele-ako Bata: Namijin gangar bata.
  4. Kudi Bata: Ɗan gangar bata.

Manazarta


Adedeji F. (2005). Classification of Nigerian gospel music styles. An ciro daga a shekarar 2020, daga shafin: https://www.revistas.usp.br

Adenike I.A. (2014). The media, the reconstruction of drumming, and the tradition of the dùndún and the bàtá ensemble of the Yorùbá in South Western Nigeria. Delta State University, Nigeria.

David J. F. (2018). Traditional Music Education in Nigeria: Bata Drum in Perspective. Music Unit, Department Of Faa/ Music Federal University Ndufu-Alike, Ikwo. American Journal of Humanities and Social Sciences Research (AJHSSR) e-ISSN: 2378-703X, Volume-02, Issue-09, pp-136-139. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: www.ajhssr.com

Oluga S. O. da Babalola H. A. L. (2012). Drummunication: The Trado-Indigenous Art of Communicating with Talking Drums in Yorubaland. Global Journal of Human Social Science, Arts and Humanities, Volume 12, Issue 11, Version 1.0. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://globaljournals.org/GJHSS_Volume12/5-Drummunication-The-Trado-Indigenous.pdf.

Masarautun Ƙasar Yarabawa

Ijoba ile Yoruba
Kingdoms of Yorubaland




Kaɗe-Kaɗe


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub